A wannan shiri na Dadin Kowa kashi na 70, Gimbiya ta shiga halin kaka-ni-kayi inda Rabi Nas tace lallai sai ta bar gidanta ta koma sansanin gudun hijra . Wai shin yaya rayuwa zata kasance ma GIMBIYA? Yarinyar da take cikin tsananin bukatar taimako. A wani bangare kuma, Malam Malami zai ziga Dantani mai Shayi ya koma wurin Alawiyyah ya cigaba da gwagwarmaya duk da cewa Nuhu Kansila ya yi masa fintinkau.